5 Satumba 2021 - 10:15
​Lebanon: Shugaban Majalisar Koli Ta ‘Yan Shia A Kasar Lebanon Ya Rasu

Kafafen yada labarai na kasar Lebanon sun bada labarin rasuwar shugaban majalisar koli ta ‘yan Shi’a a kasar, wato Sheikh Abdul-Amir Qabalan a jiya yana dan shekara 85 a duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Labarin ya kara da cewa an haifi Sheikh Qabalan a shekara 1936 a wani yanki a kudancin kasar Lebanon, sannan mahaifinsa Mohammad Ali Qabalan da kuma kakakansa Musa Qabalan manya-manyan malaman addinin ne a kasar ta Lebanon. Har’ila yau Sheikh Abdul-Amir Qabalan ya yi karatu a birnin Najaf na kasar Iraki a gaban manya-manyan malamai na zamaninsa har ya zama mujtahiji, kuma malaman nasa sun hada da Ayatullahi Khoi, da kuma Sayyid Isama’ila Sadr.

A bangaren siyasar kasar Lebanon kuma Sheikh Qabalan ya na daga cikin malaman da suke goyon bayan bellewar kungiyar Hizbullah daga Amal, sannan baya goyon bayan maida hulda da haramtacciyar kasar Isar’ila ko sulhuntawa da ita.

342/